Archives & media

SA{ON KULAWA AKAN ANNOBAR MURAR SAR{E NIMFASHI MAI KARYA GARKUWAR JIKI – KORONA BAIROS

Daga Cibiyar Zurfin Tunani Akan CORONA VIRUS (COVID-19) ta Gidauniyar ANAP

SAM AGHA EGWU

Farkon Rubutawa: Ranar Jumu’a, 20 ga Maris, 2020.

An sake ingantawa: Ranar Talata 24 ga Maris, 2020.

 

A }asar mu Najeriya zai yi wuya ace mutane ‘yan }alilan ne suka kamu da cutar annobar murar nimfashi mai karya garkuwar jiki wadda a yanzu ta addabi duniya. Wannan hasashen ya samu ne daga la’akari da halayen mutanen mu, na duhun kai, jahilci, rashin fahimta da rashin son cigaba. Da]in da]awa sakamakon da aka samu a manyan }asashen Turai, wanda sun fi mu tsari, kayan aiki da kulawa, wanda ya nuna cewa suna da ]aruruwan masu dauke da wannan cuta duk da kulawar su, ya tabbatar da cewa baza’a rasa ta ba, a Najeriya. A Najeriya har yanzun ana amfani ne da tsohuwar hanyar binciken wanda ya kamu da cutar, wato ta bibiyan wa’yanda suka yi cu]anya da masu cutar. Ko da yake wannan hanyar bincike ta yi amfani akan cutar Ebola, amma ba dole ne ta yi akan wannan cutar ba. Dalili kuwa shine, mutane da yawa a Najeriya ba su da wayar sadarwa, kuma a wurare da yawa ba’a samun ishashen sadarwa (network), ko rashin wutar lantarki, ko kuma babu cikakken addireshin gidaje. Wannan damuwa da rashin tsari na zamantakewa ya sa, zai yi wuya a iya binciko duk wa]anda a kayi cu]anya da su. Lokacin da za’a ~ata ya na da yawa. Hakan zai sa cutar ta gama gari kafin a gano wa]anda ake nema. Wannan shi ne ya sa dole mu tashi tsaye don wayar da kan mutanen mu na bairni da }auye akan wannan Annoba. Ita Annobar murar sar}e nimfashi watau korona bairos, ta na ya]uwa ko da alamomin ta ba suyi karfi a jikin mai dauke da ita ba, saboda haka tafi cutar Ebola hadari. Cutar Ebola tana bayyana kanta cikin hanzari, kuma ana ]aukar ta wajen shafar jikin mutumin da yake ]auke da ita, ko kuma ta jini, tari da kuma cu]anya kai tsaye da mai dauke da ita. Amma tana saurin bayyana, saboda haka akan saurin gane wanda ya kamu kuma a ]auki mataki, ba kamar cutar murar sar}e nimfashi ba. Ko da yake ita ma ta na ya]uwa ta wajen taba baki ko hanci da idanu da kuma ta feshin kwayoyin cutar daga baki idan mai cutar ya yi atishawa ko tari. Yana da mahinmanci a sani cewar har yanzu ba’a fahimci mataki na biyu na watsuwar ita wannan cutar ta murar sar}e nimfashi ba. Wannan shi ya sa ake ta garga]i akan kulawa da kuma killacewa don a yanzu su ne hanyoyin da aka sani na ya]uwar wannan cuta. Wa]annan hanyoyi na kulawa, su ne masu binciken }asar China suka tabbatar a matsayin hanyoyi na farko da za’a kula dasu wajen rage ya]uwar wannan cuta. {asar China ita ce }asa ta farko da ta kamu da wannan cuta kuma ta rasa rayukan mutane da yawa, kafin su farga. A dalilin haka ne binciken mutanen }asar China ya zamo abin amfani, kuma abin a maida hankali a kansa.

MUTANEN DA SUKA KAMU DA CUTAR A KWANAKIN FARKO

Wannan cutar, tana da yanayi na sa~anin kama. Har yanzu ba’a fahimci kamanninta duka ba. Abinda aka sani na kamanninta baifi kashi guda ba cikin goma, sauran tara bisa goma, suna boye, kamar {an}ara a cikin Kogi. Idan muka yi la’akari da dinbim yawan jiragen sama da suke sauka a {asannan, daga dukkanin }asashen da suka kamu da annobar murar sar}e nimfashi, wasu masu ]auke da annobar, amma bai fara tasiri akan su ba, za su iya tsallake jami’an tsaron filin jirgin sama su wuce. Idan akayi la’akari da ciniki da kasuwanci da gine- 2 gine da ake yi kota-ko-ina a Najeriya, ba sai an samo masanin kididdiga ba, kafin a fahimci cewa tabbas }wayar cutar ta watsu a dukkan {asar nan. Lokacin da aka tantance mutum daya mai ]auke da ita, ya riga ya harbi mutum biyar zuwa goma, ba tare da sanin sa ba, kuma alamomin ba zai nuna a kan su ba, sai bayan kwana goma sha hudu. Wanda suka harbu ba dole a san su ba, kuma su ma za su iya harban mutane biyar zuwa goma. Cikin sati biyu, mutum ]aya zai iya sanadin ya]awa mutane hamsin (50) zuwa ]ari (100). Wannan hasashen zai iya zama da kuskure, amma kuma zai iya kasacewa gaskiya. A dalilin haka ne mu ke zaton ]aruruwan mutane sun kamu da wannan cutar a Najeriya. A }asar Biritaniya (Ingila) mun kasance muna wa }asar Italiya da }asar China dariya saboda muna tunanin yanayin rayuwar su ne ya janyo ya]uwar wannan annoba. Ko Shugaban Biritaniya bai ]auke ta da mahimmanci ba da farko, lokacin muna da mutane da ba su wuce goma (10) ba. Saboda wannan sakaci, bayan sati ]aya sai cutar ta ya]u fiye da tunanin mu don kuwa kusan mutune ]ari hudu (400) ne suka kamu. Yawan mutanen da ke mutuwa a kullum ya }aru daga mutane saba’in da ]aya (71) zuwa ]ari da ishirin da bakwai (127). Masana sun tabbatar da cewa kusan mutane dubu hamsin (50,000) ne su ka kamu da wannan cutar a duniya, yawancin su sun fito daga }asashen China, Italiya, Iran da sauran su. A }asa da sati uku (3), a yau mutane dubu shida da ]ari da tamanin (6,180) sun kamu, ya yin da mutane ]ari uku da hamsin da biyar (355) suka mutu, kuma mutane ]ari da talatin da biyar (135) suka warke. A Italiya kuwa, a cikin kwanaki uku (3) annobar ta }aru daga kashe mutane ]ari biyar (500), zuwa ]ari shida (600), har ya zuwa ]ari bakwai (700) a rana. Jimillar annobar a yau, shi ne: masu ]auke da ita sun kai mutane dubu hamsin da ]ari hu]u da goma shatakwas (50,418) wanda suka mutu kuma sun kai dubu shida da saba’in da bakwai (6,077) sannan kuma mutane dubu bakwai da ]ari hu]u da talatin da biyu (7,432) sun warke. Yawan rasuwa a {asar Italiya yama zarce na {asar China saboda sun yi jinkiri wajen hana zirga-zirga. Har yanzu, Amurka na sakaci, suna jinkirin hana zirga-zirga. A cikin mako biyu kawai mutum Dubu arba’in da ]ari biyu da saba’in da ]aya (45,271) suka kamu, mutane ]ari biyar da tamanin da biyu (582) suka mutu, sannan mutane ]ari biyu da chasa’in da biyar (295) sun warke. Ba gaskiya ba ne cewa Ba}a}en fata na da garkuwa na kariya daga wannan annobar. Ya kamata a gane cewar ba maganar launin fata ba ne, kamar yadda Turawa fararen fata su ke kamuwa kuma suna mutuwa, haka ma Ba}a}en fata ke kamuwa a nan {asar Biritaniya, haka kuma yanzu a Najeriya. Kuma ba gaskiya ba ne, cewa yanayin zafin }asar mu ya yi yawa, ko da yake yanayin zafi na ragewa kwayar cutar karfi. Amma Yanayin zafin yana ma kasheta ne Kafin ta shiga jikin ]an Adam. A lokacin da na ke wannan rubutun, Najeriya tana da mutane talatin da bakwai (37) masu dauke da cutar, mutum ]aya (1) ya mutu, mutane biyu (2) sun warke wanda ya kawo jimmilar wanda suka kamu zuwa arba’in (40). Wannan ya nuna cewar a cikin sati guda an sami mutane arba’in sun kamu, daga mutum guda ]aya na farko. Samun masu dauke da annobar su arba’in (40) cikin sati ya na nufin za’a iya samun fiye da mutum dari (100) da cutar ta kama su. Wato zai iya yiwu Najeriya na da ]aruruwa yanzu, kuma idan ba ayi wani abu da wuri yanzun ba, mutane dubbai zasu iya kamuwa, daga nan kuma ta watsu duka gari. Wannan cutar ba za ta tsaya ba, sai mun tsayar da ita. Zamu tsayar da ita ne kuwa in mun zauna waje ]aya

Dalilai uku da zai yiwu su, su ka sa, ba ma samun, karin alkalumman masu kamuwa da cutar su ne:

i. Gwamnati na taka tsan-tsan don ka da ta tashi hankalin jama’a.

ii. Rashin samun bayanai akan lokaci, yana kawo tsaiko saboda raunin iya aikawa da rahotanni na hukumomin lafiyar mu.

iii. Ma fi mahimmanci kuma shi ne, rashin yin gwajin cutar, saboda rashin wadatan na’urorin yin gwajin. 

AUKAN MATAKAN GAGGAWA

Mutanen Najeriya za su sami kansu cikin matsananciyar damuwa idan wannan cuta ta samu wajen zama, saboda rashin kayan kula da lafiya, da wadatattun ma’aikatan jinya. {asashe kamar Italiya na shan wuya wajen shawo kan wannan cutar, saboda sakacin da su ka yi da farko, har ana aika musu agajin likitoci daga {asar China da Cuba don su taimaka. Zai fi matu}an dacewa a yanzu a bada umurnin bada tazara tsakanin mutane wajen mu’amala da juna, da kulle garuruwa tun yanzu, don a rage ya]uwar cutar. Dole ne mu ]auki mataki cikin gaggawa. Ghana, Uganda, Rwanda da Zimbabwe duk {asashen Afrika ne da su ke ]aukan matakai da wuri, domin su hana ya]uwar cutar. Har yanzu Uganda ba ta sami wanda ya kamu da cutar ba, amma tuni sun rufe filayen Jiragen saman su da wuraren chu]anyar jama’a, kamar Majami’u da Masallatai da Makarantu da sauransu, domin su hana annobar shiga {asar su. Kasar Zimbabwe su har ‘Yan Sanda su ka tura, zuwa Majami’u da Masallatai, don su hana mutane taruwa. Ghana da Rwanda suna ]aukan matakai cikin basira. A Ghana duk fasinja masu shigowa ana ke~e su, na sati biyu don asan halin da suke ciki. A Rwanda, suna amfani da sinadarin tsabtace hannu don kare jama’a daga ya]uwar cutar.

NAJERIYA NA CIKIN JERIN {ASASHEN DA ZA SU FI SAURIN KAMUWA

Masu nazari, na cewa India da Najeriya, za su zama {asashen da za su fi kamuwa da wannan cutar. A Najeriya akwai wasu dalilai da zasu dagwula al’amarin. A cewar Mr. Atedo Peterside, wanda ya kafa bankin Stanbic/IBTC, a tattaunawar sa da gidan talabijin na Channels TV, akwai dalilai guda hudu da suka sa rikita-rikitan wannan cuta mai sar}e nimfashi zai tsananta a duniya:

1. YAWAN JAMA’A: Najeriya ta na da yawan jama’a, musanman a unguwannin matalauta na biranenta. Za ka ga motocin haya cike da fasinja, idan aka sami wani mai ]auke da cutar, yawancin wanda su ke ciki sai sun kamu. Makamancin haka ne ya faru da ]an {asar Italiya da ya shigo, kuma yana kame da cutar, direban day a ]auke shi daga tashar jirgi shi ya fara ]auka. Wannan ciwon ya sha bambam da ciwon Ebola, wanda shi dole ne sai an hada jiki da jiki kafin a ya]a ta. Kasancewar haka, da zarar mutum guda na da cutar kuma ya shiga mota da wa]anda basu da ita, akwai tabbacin zai ya]awa na cikin motar. Haka kuma duk wa]anda suke cikin motar za su je su ya]awa wa]ansu a gidajensu, Masallatai, Majami’u, wajen aiki da Makaranta. Ba da sanin su ba, su kuma, za su cigaba ya]awa a wuraren da suke zuwa a gari. Muddin aka bari yanayin ya kai haka, zai wahala a kawo }arshen wannan cutar a Nigeria. Bin sawu zai iya amfani ta wajen Ebola ne kadai, wanda yana ya]uwa ne ta haduwan jikin mutum da mutum.

2. KARAYAR FARASHIN [ANYAN MAN FETUR A DUNIYA: A halin da {asashen duniya suke ]aukan matakai na rufe iyakokin su, da hana tafiye-tafiye a hanyoyi na }asa da na sama, bu}atan man fetur ya ragu kwarai. Sakamakon farko shi ne dogaron Najeriya akan ku]in shiga daga man fetur. Raguwar bu}atar man fetur a duniya ya sa farashin sa ya fadi war-was, kuma zai iya da]a fa]uwa }asa da ku]in da ake kashewa, domin ha}o shi da sarrafa shi, sannan kuma ba masu saye. Wannan ya na nufin lokacin da wasu {asashe ke fitar da ku]i da hikimomin farfa]o da tattalin arziki don ya}ar wannan annobar, mu a matsayin mu, na al’umma ]aya ba mu da ku]in da za mu kashe don kawo }arshen wannan cuta. Magunguna da kayan aikin da ake bu}ata basu a {asar nan, a yanzu haka. Ba mu da ku]in gudanar da ayyuka, ko ma na biyan albashi, saboda haka jama’a a ]ai-]ai- kun su, ba za su iya, ya}ar ta ba. Sannan yanzu ba wanda zai ba Najeriya bashin ku]i, saboda fa]uwar farashin man fetur.

3. DAIDAITO TSAKANIN LIKITA DA YAWAN MARASA LAFIYA: Ko }asashen da suka cigaba irin su Italiya, China da Koriya ta Kudu, sai da suka shiga matsananciyar damuwa, duk da yawan likitocin da suke iya duba marasa lafiya a }asashen. A Biritaniya, sun kori wasu marasa lafiya daga asibitoci, kuma suka soke yin wasu fi]a da aka shirya a baya, kafin ~ullar cuta, domin a tanadi wurin sauke masu cutar da ake tsammani. A }asar Iran yawan, mutane na fa]uwa suna mutuwa a tituna saboda rashin asibitocin da za su kula da su. Najeriya wata kila, tana cikin masu mafi karancin yawan likitoci da suke kula da marasa lafiya, kuma duk da jarumtar ma’aikatan jinyar mu, wannan annobar zai sha }arfin su, kamar yadda ya yi a Italiya, idan ba mu tsai da shi yanzun ba.

4. ARZIKI DA HADA-HADAR CINIKAYYA A DUNIYA: Ba kamar }asar China, Italiya da Biritaniya ba, Najeriya bata }era kayan aiki ko magungunan da ta ke bu}ata. Kasar China, ta gina asibitoci biyu domin kula da masu annobar a cikin sati biyu kacal. Kuma suna sarrafa magungunan su. A Biritaniya, sai da maganin rage radadin ciwon, irin su farasitamol da ire-iren su suka kare tas, a {asar. Shin kuwa gwamnatin Najeriya ta bada sautun siyo na’urorin gwaji da magunguna? In sun bada sautu, to sai ya dauki makonni kafin su iso }asar nan. Duk }asar da take yin magani sai ta gama da bu}atun ta, na ya}ar annobar cikin }asar ta, kafin ta sayar mana. Idan muka samu, aka shigo da maganin cikin {asar, to akwai kuma babbar }alubalan aikin fito, a tashoshin jiragen ruwan mu, wanda suke cunkushe. Kasar China tana fiton kaya a tashoshin jirgin ruwan ta, cikin awa Ashirin da hu]u (24) kacal, amma mu yana daukan mu makonni.

WASU HALAYYAN ‘YAN NAJERIYA

‘Ýan Najeriya na da halaye da suka danganci jahilci da taurin kai da rashin bin doka. Wa]annan halaye, na da ha]ari so sai, don za su hana biyayya ga }a’ídodin da aka sa. Yin hakan kuma zai jawo }ara ya]uwar wannan cuta, musamman cikin talakawa na birni da }auyuka.

i. RASHIN KISHIN KAI NA SHUGABANNI Rashin kishin kai da rashin kishin }asa na daga cikin dalilan da yasa abubuwa basa tafiya daidai a Najeriya. Shugabanni basa ]aukan matakai na kulawa don cigaban }asa da kyautatawa talakawa, sai dai domin amfanin kansu. Wannan ]abi’ar ce ta kassara aikin gwamnati, ta kuma hana ruwa gudu a ayyukan yau da gobe na cigaban {asar nan. Ya kamata ace shugabanni sun koyi darasi daga wannan damuwa don kuwa ta kange su daga samun damar fita zuwa asibitocin }asashen Turai. Mai yiwuwa sai sun fara rasa rayukan su a dalilin wannan cutar sannan za su ko yi darasi. Wannan kuma zai zamo ihu bayan hari, wato ba’a koyi komai ba ke nan.

ii. SAKACI: ‘Yan Najeriya kamar wasu irin mutane ne, da zasu iya ganin jirgin }asa da ya nufo kansu zai ka]e su, su mutu, amma ba su damu ba. Sun maida shi abin almara, wato kamar abun da ba zai kasance gaskiya ba. Wannan shi yasa, har yanzu wasu makarantu, majami’u da masallatai wadanda su ne mafi sau}in hanyoyin ya]a wannan cuta, har yanzu an barsu ba’a rufe su ba, a lokacin da nake rubutun nan. Irin wannan sakaci shi zai kai mu ya baro mu, don kuwa zai hana mu koyan darasi daga manyan }asashen duniya da su ke cikin tsananin damuwa a yanzu.

iii. SAKARCI: ‘Yan Najeriya ba sa son fa]awa kan su gaskiya, kuma sukan aikata abun da zai zo ya dame su daga baya, wanda suke kira wayewa. Mutum mai ]auke da cutar zai gwammace ya zauna cikin ta don sakarci yana ya]a wa wasu, a maimakon ya bada ha]in kai, a yi masa magani. Har yanzu wasu daga cikin wa]anda suka kamu suna cigaba da harkokin su da abokai da ‘yan mata; iyalai kuma na ta runguman junan su. Ba su fahimci mahinmancin killacewa ko bada tazara tsakanin mutane ba, don neman kariya. A wasu {asashe mutane suna }o}arin aiki da tunani, da zaran an yi bayani, kowa ya fahimta duk za su yi aiki da shi. Kamar umarnin a zauna a gida, da yawa daga cikin }asashen Afirka ma duk sun fahimta kuma sun bi. ‘Yan Najeriya kuwa, suna tunanin 5 basu iya barin zuwa kasuwancin su, da masallacin su, majami’un su, ‘yan Matansu, da wuraren sha}atawar su, ko kuma wani banzan ra’ayin munafincin su da kuma wajen ya]a labaran }arya.

iv. YA[A LABARAI DA RA’AYIN ZARGI NA {ARYA: Tsananin damuwa da labaran }arya yana dagula al’amurra. Ana ta ya]a }arairayi da labaran }arya. Wani ya bada shawara cewa: kar ku sa, mayanin kare fuska saboda wani barawo zai iya sa guba, ko wani sinadarin da zai sa mutum ya suma, don ya yi mashi sata. Ko kuma a ce Bill Gates, yana son ya sa muku wani kwayan halitta da sunan rigafi don ya rage yawan jama’a. Amma fa kar ku fara ku kar~i mayanin fuskar wani, saboda kar su ya]a muku Cutar.

v. RASHIN SANI: Takaitaccen ilimi da kuma jahilci yana }ara wahalar fahimtar da jama’a. Mutane ba sa iya karatu, ko kuma suna karatun da takaitaccen fahimta. Yana bukatan a fassara masu ta harshen da zasu fahimta, kuma a isar musu da bayanai.

vi. CHAMFI: Chamfi da kansa ma }wayar cutar ne. ko da yake, mun san daga inda cutar ta fito, amma a Najeriya, mutane da yawa na kiran ta Cutar karshen lokaci; wasu za su yi hanzarin zuwa wajen Pastor, ko Mallam ko Boka domin a yi musu fassaran hakikanin ta. Wannan ba }aramin ha]ari ba ne kuma dole a }alubalance shi, in ana son a ci }arfin wannan Cuta.

vii. ADDINI: Yakamata a rufe masallatai da majami’u. Amma abin mamaki Shugabannin addinai su ne ke gayyatar mutane don su yi masu addu’a akan ‘}arshen lokaci’ ko kuma su ce Ruhu Mai tsarki zai kare ka, da kuma cewa gwajin imanin mai bi ne kawai. Wannan zai sa mutane su zauna tare, su dayawa na tsawan lokaci, ana wa}o}i, ana fitar da yawu da tururi daga bakuna. Wannan shi ne hanya mai sau}i, na ya]a wannan kwayar cutar ta cu]anya kurkusa. Shin mutane ba za su iya yin addinin su a gida ba? Shin littafan mu na addini basu garga]e mu akan annoba ba ne? Wasu daga cikin umarnin gwamnati na kwanan nan, shi ne kada taron jama’a su wuce mutum hamsin (50), a cikin majami’u ko masallatai. Biyayya ga wannan doka ko ka]an, bata hana yin addini ba, ta ma kyautata shi ne. Ya kamata Shugabanni, ako ina cikin {asa su }arfafa wannan doka da }arfin mulki. Abin da ya dace, shi ne, a dakatar da duk harkoki a majami’u da masallatai.

viii. TARON JAMA’A: Wannan lokaci ne da ya kamata, a dakatar da duk taron zumunci: daurin aure, janaza, tarzoma, sha}atawa, zaman mashaya da tashoshin mota da sauran su. Idan ba za ku iya ]aga aure ko janaza da bukin mutuwa ba, to kada a tara mutane da yawa, a takaice ka da su wuce mutane ashirin (20), kuma su tabbatar sun kiyaye da dokokin }asa. In har baza’a bi dokaba, to a hana taron koda kuwa na bauta ne.

ix. JIJI DA KAI, NUNA ISA DA RASHIN YARDA: Wannan ya na daga cikin halin da ke damun ‘yan Najeriya. Saboda jiji da kai da nuna isa, ]an Najeriya zai ga gaskiya ya }i yarda da ita; ko kuma su ce abin da Allah ya rubuta babu mai share wa. Ko kuma su ce an lullu~e su da jinin annabi Isah, saboda haka babu abun da zai same su. Duka addinai suna jingine tunanin hankali da kimiyya, akan wani fata maras tushe. Idan Fafaroma zai iya }ulle Majami’ar St.Peter, kuma hukumar Saudi Arabia zata kulle Ka’aba, bai kamata a bar Limamai da Fastoci su rinka barazana ga rayuwar al’umma ba, akan imani na karya cewa suna da kariya daga annoba, ko kuma su rin}a tunkarar mutuwa da gangar.

x. TALAUCI DA RASHIN AIKI: Talauci da rashin aiki ya kasance babbar matsala a rayuwar ]an Adam. A dalilin haka, ya zama dole masu hali su taimaka wa marasa wadata. Idan hakan bai samu ba, dole ne marasa wadata su nemi mafita, ko kuma su zauna agida har sai sun mutu. Kasancewar an dakatar da zuwa aiki na gwamnati da masana’antu, da kuma ‘yan-kasuwa, jama’a zasu shiga cikin tsanani, musamman wa]anda basu da jari mai karfi. A dalilin wannan annoba ta murar sar}ewar 6 nimfashi, farashin ]anyan man fetur ya karye a kasuwar duniya. Wannan ya sa ku]in shigowa na kasa ya ragu, wanda zai sa gwamnati ta gaza biyan maáikata da ‘yan Kwangila. Maganar gaskiya, ka]an ne daga cikin ‘yan Najeriya zasu iya kwanaki goma sha hu]u, zaune a cikin gida ba tare da sun fita, don neman abin da zasu saka a baka ba. Abin damuwa shi ne cewar wannan annoba, tana bukatar kebewa ta watanni biyu zuwa uku don samun sau}i, wanda ya }arfafa bu}atar masu hali su hanzarta kai gudunmuwa don marasa wadata, su iya zama cikin gida na tsawan kwanakin da ake bu}ata.

xi. {ARANCIN ABINCI: Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya talakawa ne wanda su ke ciyar da kan su da }yar. Da yawan su sai sun fita su ke samun abin da za’a ci a ranar. A manyan }asashe kamar Ingila (United Kingdom), kusan duk mutanen zasu iya zama cikin gida na tsawan kwnakin da ake bu}ata. Wannan kuwa ya faru ne saboda, }arfin arzikin wa]annan }asashe da cigaban su, da kuma taimakawa da kyautatawar gwamnatocinsu. {asar mu Najeriya bata da irin wannan }arfin arzikin, kuma shugabannin mu basu da kishi da kulawa. A dalilin haka zai yi wuya talakawa su zauna a gida na wannan tsawan lokaci, in ba su sami agaji daga gwamnati ko masu hali ba. Halin rashi zai sa, dole talakawa su fita, zuwa gona, ko kuma kasuwa, don neman abinda za su kawo wa iyali. Ta wannan hanyar ne kuma wannan cutar zata sami masu ]aukanta da kuma ya]ata zuwa wasu wurare cikin }asa da }auyuka. Wannan yasa dole aja kunnen gwamnatin {asa da na jahohi da }ananan hukumomi, da su tallafawa marasa }arfi don su zauna agida. Gwamnati na iya amfani da Soja ko makamantan su don ganin wannan tallafawa ta isa zuwa wa]anda ya kamata su samu. Bai kamata gwamnati ta yi wasa da wannan cuta ba, don masu mulki sunfi kowa sanin ~arnar da cutar takeyi a manyan }asashe da suka fi mu shiri na kayan aiki, kuma suka fi mu }arfin arzi}i. Bai kamata a bari wannan cutar ta shiga }auyukan mu ko kuma sansanin ‘yan gudun hijira ba, don kuwa ba za mu iya kawo }arshen ~arnar ta ba.

xii. RASHIN BIN DOKA: Tsananin rashin aiki zai iya sanya matasa bijirewa da fan]arewa doka. Damuwar rayuwa ma duk tana iya tunzura jama’ar gari musamman matasa don neman hanyoyin da za su kyautata rayuwar su. Wannan ya sa dole ne gwamnati ta hankalta ta kuma shirya wa wannan cutar domin kuwa ba }aramar masifa take tare da ita ba, kuma za ta iya haddasa rashin bin doka da tozarta gwamnati.

MATAKIN KAWO {ARSHEN CUTA MAI SAR{E NIMFASHI

Masu magana sun ce rigakafi yafi magani. {asashen da suka cigaba a duniya kamar su China da Iran sun rasa mutane masu yawa a dalilin watsuwar wannan cuta. Bai kamata Najeriya ta yi wa wannan cuta ri}on sakainar kashi ba, domin ko kusa Najeriya ba ta da shiri na kula da lafiya mai }arfin da ya kama wa]an can {asashe. {asar Turai ta Ingila na cikin manyan {asashe na duniya, wajen arzi}i da tsari da kuma kulawa da lafiyar ‘yan }asarta, duk da haka Shugaban {asar (Prime Minister) yayi i}irarin cewar sai anyi namijin }o}ari za’a iya samun sau}in wannan cutar a cikin watanni uku. Ya kuma }ara da cewar, samun sau}i bashi ne kawo }arshen ta ba, Sai an }ara da matsanai cin kulawa wajen hana zirga-zirga, musamman tsakanin {asashe. Za’a sami maganin ta ne kawai idan duk }asashe sun yi, biyayya ga dokokin da aka tsaya a kai, kuma kowa ya tsaya cikin }asar sa na tsawan lokaci. Wannan cuta mai sar}e nimfashi, ta na da kamanni irin na zazzabin cizon sauro, domin kuwa ko da mutum ya warke zai iya sake kamuwa, idan ya ha]a jiki da wanda bai gama warkewa ba. Wannan ya faru a }asar China, ya kamata wannan ya zamo darasi ga Najeriya da sauran }asashe na Afirka. Wannan damuwar daban ta ke da cutar Ebola, babu }asar da zata zo don ta kawo ]auki ga wata }asar, don gudun kada su sake kamuwa da cutar. }asashen Afirka dole su farka, su tashi tsaye, don su kare }asashen su daga wannan annoba. Bincike ya nuna hanya mafi sau}i na kawo }arshen wannan cutar, shi ne nisantar juna da kuma }aurachewa, musamman in mutum ya nuna alamun kamuwa da cutar. Sai fita, ta zama dole, sannan mutum zai fita, kuma kafin ya fita sai ya ]auki duk matakai na kare kai. Wannan shine 7 matakin da duk }asashen Turai suka ]auka, a kan haka ne Shugaban Ingila da na Italiya suka rufe duk tafarkin zirga-zirga ta shiga ko fita daga cikin }asashen su. Wa]anda aka ba wa damar zirga-zirga su ne kamar ma’aikatan lafiya, masu bayar da magani, masu kula da manyan kantina, sufuri, kayan abinci, ruwan sha, man fetur, masu kwasar shara, jami’an soja da ‘yan sanda da makamantan su. A }asar Ingila wannan }a’idodi ana kulawa da su, so sai a makarantu inda iyaye masu zuwa ayyuka na musamman ke kai yaransu don kulawa lokacin da su ke wajen aiki. Wannan }a’idodin }asar China ta tsaya akai na tsawan watanni biyu kafin su sami sau}in wannan cuta. Duk da haka ba su tsaya ba, sun cigaba da kulawa bin wa]annan }a’idodin da gaskiya. {a’idodin su ne wanda su ka dakatar da sufuri na jirgin sama tsakanin }asashe, aka hana zirga-zirga tsakanin garuruwa na cikin }asa. Sannan kuma a tabbatar da duk iyalai, sun zauna cikin gidan su, kuma sun kasance cikin kwanciyar hankali da tsabta. A wayar wa da mutane kai cewar wannan ba lokaci ne na sumbatar juna ba, yawan gaisuwa, yawan jima’i da sauran yawace yawace zuwa mashaya da ragowar wajen sha}atawa. Lokaci ne, da duk iyalai za su zauna a gida, kuma ba tare da sun matsu da juna ba. Lokaci ne da za’a kasance cikin tsabta, musamman ta yawan wanke hannu da sabulu da kuma shafa sinadarin tsabtace hannu. Lokaci ne da ya kamata a sanar da yara, su rage yawan taba fuskar su, domin wannan cuta tana shiga jiki ta hanyoyi kamar su baki, hanci, da kuma idanu. Lokaci ne da za’a rage yawo a waje, in ya kama dole a gabatar da duk ayyukan da za’ayi daga cikin gida. Idan ya kama dole a fita, to sai ayi amfani da mayani don kare baki da hanci, kuma a sanya shi da kyau. Bai kamata a bar idanu bu]e a fili ba, ya na da kyau ayi amfani da tabarau don kariya. Safar hannu ta maáikatan asibiti ta na da mahinmanci wajen amfani da na’urorin zamani kamar ATM, elevator da sauransu. Ayi }o}arin yin amfani da sinadarin tsabta wajen wanke duk wuraren da hannu yake yawan tabawa. Kadan wani daga cikin iyalai ya fita ko kuma yayi amfani da abin hawa na duk gari, dole ne ya wanke hannunsa, kafin ya taba wani abu a cikin gida. Dole ne in zai fita ya yi amfani da mayani don kare fuska, kuma ya kiyayi yawan surutu da mutane a waje. A kaucewa duk mai yawaita atishawa, tari da makamantan su. A guji ]aukan wanda ba’a san tarihin lafiyar sa ba, a cikin mota don rage masa hanya, ko da kuwa ]an’uwa ne ko aboki. Da zarar haka ya faru, sai a share duk abin da akayi amfani dashi wajen tafiyar da akayi da sinadarin tsabtace lafiya. A tsabtace mota, da kayan da aka sa, kuma ayi wanka da sabulu don tsabtace duk jiki. A tsabtace }ofofin shiga da fita da duk abinda aka ]auka da hannu. A tabbatar makarantun yara na kulawa da duk }a’idodin tsabta ko kuma a dawo da yara gida. A }aurace wa duk wuraren taro na addini, aure, biki ko kuma na sha}atawa. A }aurace wa duk cu]anya da mutane a cikin mota, tashar mota, tashar jirgi da makamantan su. Yana da matu}ar mahimmanci a tsabtace duk abubuwan da ake amfani da su da hannu musamman in an fita. Wannan ya shafi kamar katin ]aukar ku]I na ATM da makamantan su. A wanke duk yanayin abinci, ko na sha kafin ayi amfani dashi, wanda ya ke bu}atar dafawa kuma a tabbatar an dafa shi sosai. Wannan cuta tana fara tasiri a cikin ma}ogoro na wani lokaci kafin ta }arasa cikin huhu. A wannan matakin za’a iya samun sa’ar cin }arfinta, in ana shan ruwan zafi domin bata son zafi ko ka]an. Yawaita shan ruwan zafi yana taimakawa wajen wanke cutar zuwa ciki kuma matsarmamar ciki na raunata ta, da hanata cigaba da rayuwa. Yana da kyau wanda ya nuna alamar kamuwa, ya yawaita kuskure baki da ruwan gishiri mai ]umi, za’a iya yin sirache na ruwan zafi a lullube kai da mayafi, ana jan numfashi mai tsawo na wani lokaci don ]umin ruwan ya raunana cutar tun a ma}ogoro. Irin wannan kulawar yakamata aringa yiwa rayuwa a kowane hali, duk abinda ya zo daga waje a tabbatar da tsabtar sa, kafin ayi amfani dashi. Wanda ya kamaci a sake bashi tsoro da wuta, a tabbatar anyi. Wanda za’a jefar a shara ayi cikin hanzari sannan kuma a wanke hannu kafin a ci abinci ko, a kama wani abun amfani.

KILLACE MARASA GATA, MARASA LAFIYA DA KUMA TSOFAFFI 

Masu yawan shekaru kamar daga Arba’in da biyar (45) sunfi kasancewa cikin damuwa idan sun kamu da wannan cutar; yara su kan samu sau}i cikin ]an lokaci. Wannan ya na faruwa ne saboda yawancin tsofaffi suna da wasu cututtuka da suke da ala}a da yawan shekaru. A dalilin haka, duk masu yawan shekaru su na bu}atar kulawa ta musamman. Ya kamata a killace su daga ragowar mutane, musamman yara wa]anda su ka kamu da cutar. Babban jahilci ne, ace wai cutar ta tsofaffi ce banda yara. Dalilai guda Uku suka sa dole matasa su kula da wannan cuta Dalilan sun ha]a da:

1. Kamar ko wane ]an Adam mai }ananan shekaru za su iya kamuwa da wannan cuta. Idan hakan ya faru cutar zata iya raunana hanyar ]auka da fitar nimfashi (Huhu) sannan ya zamanto rayuwa bazata yiwuba sai da shan magani, har }arshen rayuwa. Wannan zai iya gurgunta rayuwar matasa ya kuma cutar da kasa.

2. Saboda yanayin matasa, za su iya ya]a cutar cikin ]an lokaci, zuwa ga abokan su, iyayensu da ragowar ‘yan’uwa. Ta wannan hanyar ne cutar ta ya]u a kasar Italiya kuma ta bazu cikin ]an lokaci.

3. Yana da mahimmanci a kula da tsofaffi, marasa hali da marasa lafiya, kuma kada a yarda su kamu da wannan cuta.

MASU MULKI DA MASU ARZIKIN {ASA

Ya kamata masu mulki su yi amfani da }arfin su na mulki, su tabbatar da mutane su killace kansu. Hanya mafi sau}i ta cimma wannan }udiri kuwa itace, in an taimakawa marasa }arfi da ku]i, abinci da kuma tsaro. A Najeriya masu mulki na {asa da jihohi sun yi iya }o}arin su na ba da umarnin hana zirga-zirga, da kuma rufe wuraren aiki da makarantu da wuraren sha}atawa. Wannan ka]ai ba zai isa ba, sai an }ara da wayarwa mutane kai, don su cigaba da kulawa kuma su gaggauta sanar da shugabanni duk chanji da su ka gani a jikin su. Wannan }o}arin na bu}atar taimakawa, na masu hali, manyan ‘yan kasuwa masu zaman kansu da ragowar masu kishin }asa. Yana da mahinmancin a jaddada bu}atar taimakawa da abinci don marasa }arfi su iya zaman gida na wannan dogon lokaci ba tare da sun wula}anta ba.

WAYAR DA KAI

Cuta mai sar}e nimfashi, wato korona bairos, gaskiya ce kuma ya kamata jama’a su kula. Wannan }asida gamayya ce ta Gidauniyar Anap (ANAP FOUNDATION, COVID- 19 THINK TANK) ta buga kuma tana kiran duk wanda ya samu ya yi amfani da duk abinda yake iyawa don wayar wa jama’a kai. Ya kamata shugabannin addini, siyasa, sarakunan gargajiya, masu arziki da masu ilimi na zamani,su tashi tsaye wajen wayar da kan mutane, musamman wa]anda suke karkara. Har yanzu wannan cutar ba}uwace, kar mu yadda ta samu gindin zama, domin {asar mu bata da }arfin arzikin da zata iya tunkarar cutar. Yakamata mu farka daga barci, yakamata mu daina tunani cikin jahilci. Riga kafi ya fi magani.

FASSARAR CEDDERT, ZARIA